Jami’an Hukumar NDLEA ta Kama Dala Miliyan 20
Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA), sun kama dala miliyan 20 da take zargin na boge ne a Abuja.
Read Also:
Wata sanarwa daga hukumar a yau Lahadi ta ce jami’n sun kama kuɗin ne ranar Juma’a yayin aikin duba ababen hawa a kan hanyar Abaji zuwa Lokoja bayan ta taso daga jihar Legas.
Hukumar ta ce an kama direban motar, Onyebuchi Nlededin, mai shekara 53.
Kazalika, an kama tarin ƙwayoyi ranar Alhamis yayin wani samame a yankunan Kabusa da Dei Dei da Tora-Bora da ke ciki da kuma kewayen birnin na Abuja, a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.