‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Kansila Tare da Mutane 2 a Jihar Kaduna

 

Wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a anguwar Mai Taro da ke karamar hukumar Sabo ta jihar Kaduna.

Maharan sun kuma sace wata mata tare da kansilan sannan suka kuma yi awon gaba da wani a unguwar Dankande.

Sai dai zuwa yanzu rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar bata tabbatar da harin da aka kai a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, ba a hukumance.

Jihar Kaduna – Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun yi awon gaba da kansilan gudunmar Garu da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Alhaji Sabitu Ahmad, da wasu mutane biyu.

An tattaro cewa maharan sun farmaki yankin Anguwar Mai Taro inda kansilan yake da zama sannan suka yi awon gaba da shi tare da wata mata a unguwar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta.

Yan bindiga sun sace kakakin kansilolin karamar hukumar Sabo ta jihar Kaduna

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa, an kuma sace wani mutum guda a Unguwar Dankande da ke karamar hukumar ta Soba a ranar Juma’a, 18 ga watan Agusta.

Wani mazaunin yankin mai suna Lawal Sani ya sanar da jaridar Aminiya cewa Kansilan da aka sace shine mai magana da yawun kansiloli a yankin.

Martanin rundunar yan sanda

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ba domin baya amsa wayarsa kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba.

Sai dai kuma, mai magana da yawun Gwamnar Jihar, Mohammmed Lawan Shehu ya ce har yanzu ba a sanar da shi lamarin ba a hukumance.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com