Jami’an NDLEA Sun Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi a Jahar Legas
Jami’an NDLEA sun kama wani dillalin miyagun kwayoyi a wani coci da ke Ojudu a Legas.Lega
Mr Femi Babafemi, kakakin NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
An kama Stephen Ikeanyionu ne bayan bincike kan miyagun kwayoyin da aka kama a filin tashin jirage na Legas.
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta kama wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne da ya yi yunkurin fitar da hodar ibliss wato koken da hero*n da ganyen wiwi mai nauyin kilo gram 69.65kg zuwa Birtaniya.
The Cable ta rawaito cewa mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani coci da ke Legas.
Ya ce an gano wanda ake zargin kuma ake nema ruwa a jallo, Stephen Afam Ikeanyionu, a wani coci da ke unguwar Ojodu a Legas.
Read Also:
The Guardian ta ruwaito cewa an kama miyagun kwayoyin ne a filin tashi da saukan jirage na Legas a ranar Alhamis kuma aka gano Ikeanyionwu ne ya mallake su.
Yadda aka gano Stephen Ikeanyionu
Sanarwar ta ce:
“Jami’an NDLEA sun gano dillalin miyagun kwayoyi da ake nema ruwa a jallo, Stephen Afam Ikeanyionwu, a ranar Lahadi, 15 ga watan Agustan 2021, a wani coci da ke layin Mike Ajari, Ojodu Berger, inda suka kama shi bayan ya fito daga addu’ar lahadi.”
“An kama shi ne bayan gano wasu haramtattun miyagun kwayoyi masu nauyin 69.65kg da za su tafi Birtaniya ta filin tashin jiragen sama na Legas a ranar Alhamis, 12 ga watan Agustan 2021. Wani kamfanin jigilar kaya ne aka bawa jigilar kayan, kamfanin kuma ta bawa wani direba ya kai wurin karbar kaya a NAHCO.
“Bayan kama direban, an gudanar da bincike inda daga bisani aka gano ainihin mai kayan, Stephen Afam Ikeanyionwu, kuma aka kama shi kwana uku bayan kai sumame.”