Hukumar NDLEA ta ƙona Hekta 250 na Gonar Tabar Wiwi Tare da Kama Mutane 13 a Jahar Ondo
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta ce ta ƙona hekta 255 na gonar tabar wiwi tare da kama mutum 13 a Jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.
Read Also:
Masu sharhi na cewa zuƙar tabar wiwi ya ƙaru a Najeriya a ‘yan shekarun nan duk da nasarorin da hukumar ke samu a yaƙi da ita.
NDLEA ta ce ta gudanar da aikin ne a dazuka biyar manya cikin kwana bakwai bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari cewa a lalubo duk inda irin waɗan nan gonaki suke kuma a lalata su.