Gwamnatin Sokoto ta Nemi da a Buɗe Layukan Sadarwa a Jahar

 

Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye matakin da ta ɗauka na rufe layukan sadarwa a jaharsa sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a yankin.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai, Muhammad Bello ya fitar ranar Asabar, Gwamna Tambuwal ya rubuta wa gwamnatin wasiƙa ne yana neman a ɗage rufewar da aka yi wa layukan sadarwar.

Tun a watan Satumba ne hukumar sadarwa ta ƙasa NCC ta rufe layukan salular a ƙananan hukumomi 14 na Sokoto da kuma wasu yankunan a jahohin Kaduna da Katsina da Zamfara.

“Tambuwal ya ce ya nemi a janye matakin ne saboda damuwar da jami’an tsaro suka nuna cewa rashin layin sadarwa na kawo musu cikas wajen gudanar da ayuukansu,” a cewar sanarwar.

Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da yake karɓar baƙuncin Gwamna Umara Zulum yayin da ya kai ziyarar jaje game da harin da ‘yan fashi suka kai a Gwaranyo, inda suka kashe mutum 43.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here