Bayan Gushewarta a Daji: An ga mujiya mafi girma cikin shekara 150

 

A karon farko, an hango tare da ɗaukar hoton wata jibgegeiyar mujiya shekara 150 tun bayan gushewarta a daji.

Masana kimiyyar Burtaniya ne suka yi kiciɓis da mujiyar tana shawagi a dajin Atewa na Ghana a wannan makon.

Gani na ƙarshe da aka yi wa irin wannan tsuntsuwa shi ne a shekarun 1870.

Yanzu haka ana ta yin kira ga mahukunta su mayar da yankin da aka hango wannan mujiya wurin shakatawa don kare ta.

Nau’in mujiyar na daga cikin tsuntsaye mafiya girma a duniya, inda take da alamomi na musamman da suka hadar da baƙaƙen idanu da baki mai launin rawaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here