APC ta Nemi Mai Mala Buni da ya Hukunta Shekarau, Amosun, Okorocha, da Aregbesola

 

Gwamnoni suna so majalisar Mai Mala Buni ta hukunta wadanda suka bangare.

Akwai jahohin da aka samu shugabanni fiye da daya a zaben shugabanni na APC.

Shekarau, Amosun, Okorocha, da Aregbesola suna fuskantar matsala a jam’iyya.

Abuja – Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, yana fusakantar matsin lamba a game da zaben shugabanni da aka gudanar.

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust tace an taso Mai Mala Buni a gaba, ana so ya hukunta wasu daga cikin ‘yan jam’iyya da suka shirya zaben taware a APC.

A dalilin rikicin da ake fama da shi tsakanin wasu jagororin APC na kasa da gwamnonin jahohinsu, ‘yan taware sun ja daga a zaben shugabannin jahohi.

Wani daga cikin gwamnonin jahar da aka samu shugabanni fiye da daya, ya taso uwar jam’iyya a gaba, yana so a hukunta wadanda suka raba kan ‘yan jam’iyya.

Jahohin da babu zaman lafiya a APC

An samu irin wannan rigima a Kano, Legas, Ogun, Kwara, Osun, Filato, Neja, Akwa Ibom, da Enugu.

Daga cikin wadanda ke kan gaba wajen goyon bayan wadanda ake ganin ‘yan taware akwai Ibrahim Shekarau (Kano), da kuma Ibikunle Amosun (Ogun).

Har ila yau akwai irinsu Rauf Aregbesola (Osun), Sanata Rochas Okorocha (Imo), Akinwunmi Ambode (Lagos), da Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom) A jahar Osun, bangaren Rauf Aregbesola sun kai kara kotu a game da zaben da aka shirya.

Hakan ya saba wa umarnin da shugabannin jam’iyyar APC suka yi.

Wata majiya tace gwamnoni na so a hukunta masu ja da su domin a koya wa wasu hankali yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shugabanni na kasa.

Sakataren APC, John James Akpan Udo-Edehe yace ba za su yarda a raba kan jam’iyya ba. Amma Mala Buni ya musanya rade-radin cewa an huro
masa wuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here