NDLEA ta Gana da Hukumomin ƙasar Pakistan Kan Magance Safarar ƙwayoyi
Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLE ta ce ta gana ta hukumomin ƙasar Pakistan domin gano hanyoyin da za a magance matsalar safarar ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu.
Read Also:
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukuma femi Babafemi ya fitar ƙarshen mako ya ce shugaban hukumar Bugediya janar Buba Marwa mai ritaya ne ya tura tawagar jami’an domin tattaunawar wadda ta gudana a birnin Vienna na ƙasar Austria.
”Tattaunawar da ƙasashen biyu kan safarar ƙwayoyin tsakanin ƙasahen biyu ta gudana ƙarƙashin jagorancin hukumar safarar ƙwayoyi ta duniya, ta kuma mayar da hankali ne wajen inganta harkokin sadarwa tare da musayar bayanan sirri tsakanin NDLEA da kuma hukumar hana sha da fataucin ƙwayoyi ta Pakistan’’ kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A ƙarshen ganawar ƙasashen biyu sun cimma matsaya kan yadda za su inganta haɗin gwiwa wajen magance matsalar safarar miyagun ƙwayoyi musamman ƙwayar Tramadol tsakanin ƙasashen biyu.