Atiku Abubakar ya Jagoranci Zanga-Zangar PDP a Abuja

 

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jagoranci wata zanga-zangar lumana da jam’iyyarsa ta shirya a Abuja domin nuna adawa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa Iyorchia Ayu, da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, da kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal na daga cikin waɗanda suka halarci zanga-zangar.

Ita dai jam’iyyar PDP na zargin an tafka maguɗi a zaɓen wanda ya gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu, wanda hukumar zaɓen Najeriya -INEC ta sanar da ɗan takarar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Baya ga PDP, ita ma jam’iyyar Labour wadda Peter Obi ya yi takara a ƙarƙashin ta, ta soki sakamakon zaɓen inda ta sha alwashin ƙalubalantar sa a kotu.

Sun yi zargin cewa babu adalci a zaɓen wanda aka yi amfani da na’urar BVAS.

Sai dai hukumar zaɓen Najeriya -INEC ta musanta zargin aikata ba daidai ba.

Bola Tinubu na APC wanda ya samu kashi 37 cikin 100 aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen, sai Atiku Abubakar ta biyu mai kashi 29 cikin 100.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here