NNPCL ya Sanar da Sabon Farashin Litar Man Fetur
Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.
Tuni dai wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.
Read Also:
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.
Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.
Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.
Sai dai kuma, gwamnatin tarayya ta musanta bai wa kamfanin umarnin ƙara farashin litar mai ɗin.