Rashin Tsaro: NOA za ta Kaddamar da Manhaja ta Wayar Salula Domin Taimakon Gaggawa
Darakta-Janar na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta kaddamar da wata manhaja ta wayar salula domin taimaka wa rahotannin yanayi na gaggawa da kuma barazanar tsaro.
Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron hadin gwiwa da kungiyar gudanarwar kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR) karkashin jagorancin shugaban kamfanin Mallam Yushau Shuaib a hedikwatar NOA da ke Abuja.
Da yake jawabi a wajen taron, Mallam Onilu ya ce, “muna samar da hanyoyin yin cudanya da ’yan Najeriya, kuma nan da mako mai zuwa, za mu kaddamar da app na mu, manhajar wayar salula da muke kira da Mobiliser.
Read Also:
“Application din yana da ayyuka da yawa, daya daga cikinsu yana yin bayanin ne don baiwa ‘yan Najeriya damar gano wata barazana idan suka ga daya ta hanyar sanin abin da za su duba domin sanin abin da za su bayar.”
“Wannan manhajar wayar salularmu tana da kayan aikin da kowane dan Najeriya a duk inda yake zai iya dannawa, ba da kwatanci, loda hoto ko bidiyo na damuwa kuma za mu karbi wannan kai tsaye kuma mu tura wa hukumar da ta dace don amsa da daukar mataki.”
A cikin jawabinsa na farko, shugaban na IMPR ya sanar da mai masaukin nasa irin nasarorin da kungiyarsa ta samu wajen yin aiki tare da jami’an tsaro a fannin sadarwa da dabarun wayar da kan jama’a.
Don haka kungiyoyin biyu sun amince su hada kai da hukumomin soji domin hada kan ‘yan Najeriya don tallafawa gwamnati kan yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da sauran masu haddasa fitina.