Dalilin Mayar da Wasu Ofisoshin CBN Daga Abuja Zuwa Legas – Cardoso

 

Olayemi Cardoso wanda ke jagorantar babban bankin Najeriya (CBN) ya faɗi dalilin mayar da wasu ofisoshin CBN daga Abuja zuwa Legas.

Gwamnan na CBN ya bayyana an yi wa hedikwatar bankin da ke Abuja yawa shiyasa suka rage jama’a.

Ya yi nuni da cewa cunkoson jama’an da ke hedikwatar na buƙatar a rage ta domin kada hakan ya kawo cikas ga ayyukan bankin.

FCT, Abuja – Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Olayemi Cardoso ya bayyana cewa an dauki matakin mayar da wasu ofisoshi da ma’aikata a hedikwatar bankin da ke Abuja zuwa wasu rassa ne saboda “cunkoson jama’a”.

Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira a gidan talabijin na Arise tv.

Da aka tambaye shi ko hedikwatar CBN na da cunkoson jama’a, sai ya ce cunkoson jama’an ya yi yawa.

Ya ƙara da cewa bankin na sa ran cewa matakin zai magance matsalar cunkoson jama’an a hedikwatar bankin da ke Abuja.

“Akwai cunkoso a CBN” – Cardoso

A kalamansa:

“Gaskiyar magana, duk wanda ya zo bankin kuma ya yi hulɗa zai ga cewa akwai cunkoson jama’a. Dole ne mu ga cewa za mu iya magance matsalolin da za su iya faɗowa daga wajen da yake da cunkoson jama’a.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, CBN a matsayinsa na cibiya ta ƙasa, yana da reshe a kowace jiha ta ƙasar nan.

Sai dai gwamnan babban bankin ya ce idan aka samu yanayin da ma’aikatan da ke da ƙwarewar fasaha ke zaune a wani ɓangare kawai, hakan na iya kawo cikas ga ayyukan bankin.

A cewarsa:

“Don haka wannan ya kasance ƙoƙari ne na tabbatar da cewa an mayar da ma’aikata masu ƙwarewa daga inda akwai yawansu, zuwa inda ake da ƙarancinsu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com