Olusegun Obasanjo ya Magantu Kan Bashin da Shugaba Buhari Zai Karbo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya mayar da martani ga shirin shugaba Muhammadu Buhari na karbo sababbin rance, yana mai cewa yin aro don tara bashi ga ƴan gobe babban laifi ne.
Read Also:
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a gefen wani taro a Afirka ta Kudu, Obasanjo ya ce cin bashin da ake yi sannan ake kin biyan wanda ake bin kasar na iya zama gagarumar matsala ga gwamnacin da za su zo a gaba.
Ko da yake ya ce cin bashi ba matsala bane, tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana cewa abin da zai iya zama matsala shine biyan bashin.
”Idan ana ciyo bashi don aiwatar da ayyukan da za su iya biyan kudinsu ne to wannan ba matsala bane, in kuwa don aiwatar da ayyukan al’amuran yau da kullum ne to wannan babbar wauta ce” inji Obasanjo.