Rantsar da Tinubu: Peter Obi ya Buƙaci ‘Yan Najeriya su Zauna Lafiya da Juna
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya buƙaci ƴan Najeriya da su zauna cikin kwanciyar hankali.
Peter Obi ya yi kira ga ƴan Najeriya da su zauna lafiya da junan su domin hakan ne zai kawo ci gaban da ya dace a ƙasa.
Ɗan takarar ya kuma yi kira ga shugabanni da su mayar da hankali wajen magance ɗumbin matsalolin da suka addabi ƙasar nan.
Jihar Kaduna – A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya roƙi magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya da su kwantar da hankulansu su zama masu bin doka da oda.
Peter Obi ya kuma sake nanata matsayarsa kan cewa kotu ce kawai za ta, tabbatar da sahihin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, nan bada daɗewa ba, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Read Also:
Obi wanda ya bayyana hakan bayan ya halarci wani taro a jihar Kaduna, ya ce zaman lafiya da ƙwanciyar hankali da tsaron ƙasa ya fi kowane irin abu muhimmanci, a dalilin hakan ya yi kira ga ƴan Najeriya da zama masu bin doka da oda.
A kalamansa:
“Dole ne mu ci gaba da rayuwa akan hanyar zaman lafiya, mutunta addinin kowa, mutunta sauran ƙabilu da cuɗanya da juna, wannan shine abinda ya fi muhimmanci a yanzu.”
“Mu haɗu mu samar da Najeriya mai cike da kwanciyar hankali da lumana, inda gwamnati za ta mayar da hankali wajen kula da wahalhalun da mutane ke sha.”
Peter Obi ya buƙaci ƴan Najeriya su zauna lafiya da juna
A yayin da ya ke nuni da cewa har yanzu akwai abubuwan tababa dangane da zaɓen da ya wuce, Peter Obi ya ce dole ne ƴan ƙasa su zauna cikin kwanciyar hankali sannan su mayar da hankali wajen fuskantar ƙalubalen da ƙasar nan ke ciki na rashin tsaro, talauci, ilmi da sauran su.
Ɗan taarar shugaban ƙasar ya kuma gwamnatoci a kowane matakai da su mayar da hankali wajen magance matsalolin rashin aikin yi ga matasa, talauci da rashin tsaro musamman a yankin Arewacin Najeriya, cewar rahoton New Telegraph.
Peter Obi ya ce dole ne sai shugabanni sun magance waɗannan matsalolin idan har ana son ƙasar nan ta ci gaban da ya dace.