Gwamna Masari ya Bayyana Cewa An Samu Raguwar ‘Yan Bindiga Sosai a Jahar Katsina

 

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, yace an samu raguwar ayyukan yan bindiga sosai a jahar.

Masari ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin wakilan hukumar dillancin labarai ta Najeriya ranar Lahadi.

Gwamnan ya sake jaddada cewa aikin samar da tsaro a jahar Katsina ya rataya a wuyan kowa.

Katsina – Gwamna Aminu Bello Masari, yace sam babu wani siddabaru da gwamnatinsa ta yi wajen rage ayyukan yan bindiga a Katsina, kamar yadda aminiya ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga wakilan hukumar dillancin labarai ta Najeriya (NAN) a Katsina ranar Lahadi, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Masari ya bayyana cewa gudummuwa da kowa ke bayarwa a jahar kama daga sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki wajen nemo hanyar warware matsalar shine yake haifar da ɗa mai ido.

Wane matakai gwamnatin Katsina ta ɗauka?

Gwamna Masari ya kara da cewa tun da fari ya bada umarnin duk mutanen dake cikin daji waɗanda ba ruwansu da aikata laifuka su dawo cikin gari.

Masari yace:

“Na ba da umarnin cewar dukkan mutanen kirki da ke zaune a dazuka su fito su shiga cikin sauran al’umma a kauyuka da manyan garuruwa da birane don gudun yi musu kudin goro.”

“Saboda haka, yanzu ba mu da sauran mutanen da ke zaune a daji. Duk wanda ka gani a daji yanzu to ko dai dan bindiga ne ko kuma bata gari.”

“Hatta tsofaffin da har yanzu suke cikin daji su ma ’yan bindiga ne wadanda ke fitowa su aikata ta’asa sannan su koma, mun cimma nasara sosai wajen magance matsalar tsaro a Jaharmu”.

Gwamnati zata ginawa yan gudun hijira gidaje

Gwamna Masari ya kara da cewa gwamnatinsa zata gina gidaje domin samar da muhalli ga waɗanda lamarin rashin tsaro ya raba da gidajensu.

Ya kuma kara jan hankali cewa tabbatar da zaman lafiya a faɗin jahar Katsina alhaki ne da yake kan kowa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here