Gwamna Matawalle ya Bayyana Cewa Babu Ranar Maida Sabis a Zamfara
Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara, ya bayyana cewa babu ranar maida hanyoyin sadarwa a jaharsa.
Matawalle yace gwamnatinsa zata cigaba da tattaunawa da hukumomin tsaro lokaci bayan lokaci domin jin halin da ake ciki.
Gwamnatin Katsina ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumi 13 daga cikin 34 dake faɗin jahar.
Zamfara – Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, yace datse sabis ɗin sadarwa a jahar zai cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka ci galaba kan matsalar tsaro.
Read Also:
Hukumar sadarwa (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa su datse hanyoyin sadarwa a Zamfara na tsawon mako biyu a wani mataki na daƙile ayyukan yan bindiga a jahar.
Premium times ta rahoto yadda mutanen Zamfara suke tafiya zuwa jahar Sokoto da Fintua a jahar Katsina domin kiran waya, tura sakon karta kwana da kuma harkokin kuɗi.
Hana amfani da hanyoyin sadarwa zai ƙare ne a ranar Jumu’a, amma da yake hira da gidan Radio na BBC Hausa, Matawalle yace babu ranar maida sabis.
Yaushe za’a maida sabis a Zamfara?
Gwamnan yace:
“Ya zama wajibi mu cigaba da hakuri da rashin sadarwa, saboda babban fatan mu shine zaman lafiya ya dawo kuma mutane su tsira.”
“Zamu cigaba da tattaunawa da hukumomin tsaro kuma har zuwa sanda zasu bamu tabbaci matakin zai cigaba da kasancewa.”
“Sakamakon da muke samu daga hukumomin tsaro, shine zai tabbatar da lokacin da zamu ɗage hanin.”