‘Yan Bindiga Sun Kai wa Coci Hari Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace 3 a Jahar Kogi

 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari cikin wani coci a jahar Kogi inda suka hallaka wani mutum daya.

Sun sace mutane uku cikin masu bauta a cikin cocin a yau Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

Rundunar ‘yan sandan jahar sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma ce suna bin diddigin ‘yan bindigan.

Kogi – Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jahar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da masu ibada guda uku, Punch ta rawaito.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jahar Kogi.

Lamarin ya fau duk da cewa Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jahar a matsayin mafi aminci a Najeriya.

Harin ya faru ne kwanaki bakwai kacal bayan da aka kai hari cibiyar kula da gyaran hali ta tarayya da ke Kabba; da kuma sace wasu manoman kaji guda uku a gonarsu.

An ce masu garkuwar sun kai hari cocin ne yayin da ake gudanar da hidimar ranar Lahadi.

Cocin yana kusa da babban titin Kabba-Okene.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jahar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an su na bin sawun wadanda ake zargin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here