Sheikh Noreen Muhammad Siddiq: Tarihin Rayuwarsa Har Zuwa Mutuwarsa
Da yammacin Juma’a ne Musulmin duniya suka sami wani labari mara dadi na rasuwar fitaccen mahaddacin Al-Kur’ani Sheikh Noreen Muhammad Siddiq na kasar Sudan tare da wasu mahaddata uku.
An yi jana’izar Sheikh da sauran malaman da safiyar Asabar a Khartoum, kuma abokin aikinmu Sani Aliyu ya tattauna da Khidir Sulaiman Muhammad, wanda na kusa da marigayin ne kuma sun yi karatun Al-Kur’ani a wurin malami ɗaya.
Kuruciyar Sheikh Noreen
An haifi Sheikh Noreen Muhammad Siddiq shekara 38 da ta gabata a wani gari da ake kira Farajab a cikin kasar Sudan, kuma yayi karatun allo ne a garin Khorsi a shekarar 1998, kuma shi dalibin wani babban malami ne mai suna Sheikh Makki a Sudan.
Bayan ya kammala karatun allo ya kuma ci gaba da neman ilimin addinin Musulunci a nan garin Khorsi. Ya yi shekara 20 yana neman ilimi a karkashin malamai daban-daban, amma daga baya ya zama almajirin Sheikh Makki a Khartoum, babban birni kasar Sudan.
Kira’ar Al-Kur’ani da Marigayin ya shahara a kai
Bayan ya koma Khartoum karkashin Sheikh Makki, ya koyi salon kira’arsa wadda ake kira “Kira’ar Daubit”.
Khidir Sulaiman Muhammad:
“Malaminmu ne ke da wannan salon kira’ar karatun Al-Kur’ani, kuma dukkanmu a wurinsa muke koya, inda a masallatai da yawa na birnin Khartoum da sauran sassan Sudan ake assasa karatun Al-Kur’ani da wannan kira’ar”.
Sheikh Khidir ya ce Sheikh Noreen mutum ne mai saukin kai:
“Mallam Noreen Allah ya yi masa rahama. Mutum ne wanda duk inda aka kira shi, zai hanzarta ya je. Jiya ma Juma’a shi da wasu malamai sun tafi garin Halfa domin yin da’awa ne cikin Maulidin Manzon Allah.”
Ya kuma ce ko yara kanana ya gamu da su a kan hanya suka bukaci ya tsaya ya karanta musu Al-Kur’ani, “to zai tsaya ya karanta musu da zuciya guda.”
Read Also:
Wannan halayyar ta sa ce ta sa ya shahara kuma ya sami daukaka a gurin jama’a cikin kankanin lokaci
Rayuwarsa tare da iyalinsa
Marigayi Sheikh Noreen yana da iyali, inda kafin mutuwarsa Allah ya azurta shi da matan aure hudu da ‘ya’ya takwas.
Khidir Sulaiman ya bayyana cewa: “Cikin ‘ya’yansa takwas akwai mata da kuma maza. Babbar ‘yarsa mace ce.
“Dukkan ‘ya’yan nasa na karatun Al-Kur’ani kuma marigayin ya bayyana sha’awar wasu daga cikinsu su gaje shi.”
Hadarin mota
Marigayi Sheikh Noreen ya amsa gayyatar zuwa yankin Shmaliya wato arewacin Sudan ne domin yin da’awah tare da wasu malamai huɗu a garin Halfa. Sun sami isa can kuma sun gudanar da ayyukan da suka kai su.
Rahotannin da muka samu daga na kusa da marigayin na cewa motar da Sheikh Noreen ke ciki ta yi taho mugama ne da wata babbar mota a kusa da birnin Omdurman.
An dai kai marigayin tare da sauran malaman da ke cikin motar zuwa asibiti.
“Tun da aka sami labarin mutuwarsa, mutane ba su sami barci ba saboda sun hallara a asibitin da aka kai marigayin da sauran malamai uku, wanda sai da safe aka bayar da gawarwakinsu,” inji Khidir Sualaiman.
Ya kara da cewa, “Tun cikin dare mutane suka yi ta shigowa Khartoum daga jihohin Sudan daban-daban domin su halarci janza’izar marigayin da sauran malaman da suka mutu tare da shi.”
Sauran malaman da suka rasa rayukansu a hatsarin su ne Ali Yaqoub, Abdullah Awad Al-Karim da Muhannad Al-Kinani, amma Sayed bin Omar wanda shi kadai ya tsira da ransa a halin yanzu yana karbar magani a asibiti.
Marigayi Sheikh Noreen Muhammad Siddiq ya shahara a kasar ta Sudan saboda salon kira’ar Al-Kur’ani da yake amfani da ita ke tausasa zuciyar duk wanda ya saurare ta, kuma ganin dubun-dubatan mutanen da suka halarci jana’izarsa, babu shakka duniya ta yi rashin wannan bawan da kuma farin cikin da yake ba duk wanda ya saurari kira’ar da yake yi.