Rikici ya Barke a Ribas,Ƴan Bindiga Sun Farmaki Ciyaman

 

Ribas – Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a sakatariyar karamar hukumar Ikwere da ke jihar Ribas.

An ce an samu tashe tashen hankula a sakatariyoyin kananan hukumomin Ribas bayan rantsar da sababbin ciyamomi da kansiloli ranar Litinin.

An farmaki ciyaman a jihar Ribas

Wakilin jaridar The Guardian ya rahoto cewa ‘yan bindiga sun fatattaki zababben shugaban karamar hukumar Ikwere, Isreal Abosi.

Bayan farmakin da ‘yan bindigar suka kai, an ce masu zanga zanga sun kuma mamaye titunan jihar Ribas suna nuna adawa da rantsar da ciyamomin.

Anji masu zanga zangar na cewa, “Babu Wike babu jihar Ribas, babu Wike babu sakatariya” wanda hakan ya kara tabbatar da zargin da ake yi.

Rikici ya barke a garuruwan Ribas

Hakazalika, jaridar The Punch ta rahoto cewa an samu tashe tashen hankula a kananan hukumomi da dama ciki har da Oyigbo, Khana da Obio-Akpor.

Ana ganin cewa wadannan rigingimun ba sa rasa nasaba da janye jami’an ‘yan sanda da aka yi daga tsaron dukkanin sakatariyoyin kananan hukumomin jihar.

Rikici ya barke a garuruwan Ribas Hakazalika, jaridar The Punch ta rahoto cewa an samu tashe tashen hankula a kananan hukumomi da dama ciki har da Oyigbo, Khana da Obio-Akpor.

Ana ganin cewa wadannan rigingimun ba sa rasa nasaba da janye jami’an ‘yan sanda da aka yi daga tsaron dukkanin sakatariyoyin kananan hukumomin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here