Rundunar Soji ta Fara Daukar Sabbin Sojoji, Yadda za a Cike

 

Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, rundunar sojin Najeriya ta na kokarin kara ma’aikata don dakile matsalar.

Rundunar ta sanar da daukar sabbin sojoji a wannan shekara ta 2024 ‘yan gaba da sakandare (DSSC).

Ta ce an fara cike neman aikin ne daga jiya Alhamis 18 ga watan Janairu zuwa ranar Juma’a 23 ga watan Fabrairu.

FCT, Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta sanar da diban sabbin sojoji wadanda za a dauka masu kwalin gaba da sakandare (DSSC).

Rundunar ta bayyana cewa dole masu sha’awar aikin sojan su cike bayanansu a yanar gizo kafin Juma’a 23 ga watan Faburairu.

Mene rundunar ke cewa kan daukar sojojin?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X a yau Juma’a 19 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce:

“Dama ce ga fararen hula da kuma sojojin da suke aiki a Najeriya.

“Sojojin da rundunar ta dauki nauyinsu zuwa wasu hukumomi ne kadai za a ba su kulawa.”

Karin bayani kan yadda za a cika aikin Rundunar har ila yau, ta bada yadda za a cike aikin cikin sauki ba tare da wata matsala ba.

1. Ka shiga yanar gizo kamar haka recruitment.army.mil.ng sannan ka zabi bangaren DSSC.

2. Sannan za ka cike dukkan takardu da kuma bayanai da ake bukata kamar haka:

i. Fasfo

ii. Takardun makaranta

iii. Shaidar kasancewa a wata hukuma

iv. Shaidar kasancewa dan jiha

v. Takardar haihuwa

vi. Lambar NIN sa BVN

Sannan rundunar ta ce mafi karancin shekaru shi ne 20 yayin da 40 kuma shi ne karshe, cewar Daily Post.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com