Sababbin Tuhume-Tuhume da Gwamnatin Najeriya ta Gabatar Kan Nnamdi Kanu
Gwamnatin Najeriya ta shigar da sababbin kararraki 7 kan jagoran ‘yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.
Kararrakin sun kunshi cin amanar kasa da ta’addanci wadanda suka kasance kari kan tuhume-tuhume da ake masa tun 2016.
Read Also:
Kotu ta sanar da Alhamis 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraron kararrakin.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Ibo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an kai Kanu kotu.
Jaridar Vanguard a Najeriya ta rawaito cewa ƙungiyar ta Ohanaeze ta ce bayyanar Kanu a kotu na da muhimmanci don nuna wa duniya cewa Nnamdi Kanu na ciki ƙoshin lafiya kuma za a yi masa adalci a lokacin shari’a.