Jahohin Najeriya 12 da Gwamnatin Burtaniya ta Gargadi ‘Yan Kasar da su Guji Zuwa

 

Gwamnatin Burtaniya ta gargadi ‘yan kasar da su guji zuwa jahohi 12 a Najeriya, inda ta ce akwai yiwuwar kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da ‘yan kasashen waje.

Ofishin jakadancin Burtaniya da ke Abuja ya ce akwai bayanan da ya samu cewa ana shirin kaddamar da satar ‘yan kasashen waje da sunan neman kuɗin fansa ko kuma siyasa.

Jahohin sun haɗa da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Katsina da Zamfara da Delta da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River.

Ofishin ya kuma kara da cewa an hari ma’aikatan jin-kai a wasu hare-hare da aka kaddamar arewa maso gabashin Najeriya, da suka haɗa da na garin Manguno a ranar 13 ga watan Yunin 2020.

Wani ɓangaren sanarwar ya kuma ce “yanayin tsaro ya kara tabarbarewa a arewa maso gabashin Najeriya tun 2018, kuma akwai yiwuwar sace ma’aikata ‘yan kasashen waje”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here