‘Yan Tawaye: Zanga-Zangar na Daukar Sabon Salo a Sudan
An tsaurara tsaro a babban birnin Sudan wato Khartoum, inda bangarorin masu goyon bayan sojoji da kuma masu adawa da su ke gudanar da zanga-zanga.
Daruruwan magoya bayan gwamntin riko sun cika tituna, yayin da masu goyon bayan soji ke ci gaba da zaman dirshan a harabar gidan Shugaban kasa da suka fara ranar Asabar.
Read Also:
Jami’an tsaro a Khartoum sun rufe hanyoyin da ke isa hedikwatar sojojin kasar.
Jagororin bangarorin biyu sun yi kira ga magoya bayansu da su kaucewa arangama da juna, su kuma kaucewa tashin hankali.
Kokarin Sudan na sake dawowa mulkin farar hula zalla tun bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a 2019 na fuskantar cikas, inda kasar ke fuskantar matsalolin siyasa da kabilanci da matsin tattalin arziki.