Sojoji Sun Kama Wanda Yake Samarwa da Boko Haram Takin Zamani a Yobe

 

Rundunar sojojin kasa na shashi na biyu na JTF na arewa maso yamma sun damki wani Yusuf Saleh.

Ana zarginsa da kai wa ‘yan Boko Haram takin Urea a kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam da ke jahar Yobe.

Dama gwamnati ta hana siyar da takin Urea domin ‘yan ta’adda suna amfani da shi wurin hada abubuwa masu fashewa.

Geidam, Yobe – Rundunar sojojin kasa ta sashi na biyu ta JTF a arewa maso gabas ta Operation Hadin Kai ta kama wani Yusuf Saleh, bisa zargin siyar wa da ‘yan Boko Haram din kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam da ke jahar Yobe.

‘Yan sa kai ne suka kama shi bayan samun gamsassun labarai a kansa.

An samu buhunhuna 38 masu cikin 50kg daga hannunsa na takin Urea, HQ Nigerian Army ta wallafa a Facebook.

Dama gwamnati ta hana sayar da takin Urea saboda ‘yan ta’adda suna amfani da shi wurin hada abubuwa masu fashewa. Yanzu haka ana ta samun labarai masu amfani daga bakinsa.

Rundunar OPK sun yaba wa kokarinsu inda suka yi gaggawar kama wanda ake zargin. Sannan sun bukaci a dinga bin diddikin duk wasu labarai a kan ‘yan ta’addan don mutane da dama sun wahala a hannunsu.

An tabbatar wa da mazauna yankin arewa maso gabas masu bin doka cewa shugaban sojojin kasa ya daura dammarar kawo karshen Boko Haram da ISWAP a maboyarsu.

An shawarci mazauna yankin arewa maso gabas da su cigaba da kawo labarai wadanda za su taimaka wurin sanin tushen duk wani ta’addanci a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here