Mika Wuya: Mutane 27 Sun Mutu Sakamakon Musayar Wuta Tsakanin ISWAP da Boko Haram

 

Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram da ISWAP yayinda wasu ke kokarin mika wuya.

An kashe akalla mutum 27 a musayar wuta da suka tsakaninsu.

Yan Boko Haram kwanakin nan na mika wuya ga Sojoji.

Borno – Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun karkashe juna yayin rikicin da ya barke tsakaninsu a Arewacin Abadam, jahar Borno lokacin da wasu ke kokarin mika wuya.

PRNigeria ta rawaito cewa wasu yan Boko Haram da suka shirya mika wuya sun fuskanci kalubale wajen yan ta’addan ISWAP da sukayi kokarin hanasu mika wuya.

Bangarorin biyu sun yi musayar wuta ne a unguwar Gusuriya dake garin Dumbawa.

Yan Boko Haram suna kan hanyarsu ta zuwa wajen rundunar Sojojin hadaka ta MNJTF ne a iyakan Nijar ranar Lahadi, 22 ga Agusta, 2021 lokacin da aka kai musu hari.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa kwamandojin ISWAP sun nuna bacin ransu kan yadda yan Boko Haram ke mika wuya kuma hakan ya sa suka kafa dokar kisa ga duka wanda aka kama yana kokarin mika wuya.

Majiyar tace:

“Wani mai suna Abba-Kaka, gwamnan Tumbumma, wanda ke jagorancin Marte, Abadam, Kukawa da Magumeri, ne ya jagoranci harin inda aka kwashe awanni ana musayar wuta kuma aka kashe mutum 25. cikin har da kwamandoji uku, yayinda sauran suka arce da iyalansu.”

Me ya haddasa rabuwar kai tsakanin ISWAP da Boko Haram?

Wata majiyar daban ta bayyanawa PRNigeria cewa rabuwar kan dake tsakanin bangarorin biyu ya sake munana ne lokacin da aka kashe wasu yan ta’addan Boko Haram kan wasu laifukan da basu taka kara sun karya ba, da kuma kin basu mukamai manya.

A cewar majiyar:

“An kaskantar da wasu manyan Kwamandoji da Amirai karkashin Shekau bayan sun yi mubaya’a ga ISWAP.”

“Wasu kwamandojin Boko Haram da mabiyansu sun fara shirin fito-na-fito da ISWAP ta hanyar hada kai da Bakura da Krimima da suka dade suna yakan ISWAP a Lelewa, Duwa, Wallal da Hauwa Bulumwa a jamhuriyyar Nijar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here