Fadar Shugaban Kasa na Zargin Gwamna Ortom Kan Sanadiyyar Mutuwar Mutane da Dama a Jaharsa

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, gwamna Ortom na Benue ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan a yau Laraba cikin wata sanarwa.

Gwamnati ta zarge shi da tunzura wata kabila wajen hallaka wata kabilar, wanda ya jawo mace-mace da dama.

Abuja – Fadar shugaban kasa ta zargi gwamnan jahar Benue, Samuel Ortom, da kunna wutar kiyayya tsakanin mazauna a jaharsa ta hanyar kai hari kan wata kabila wanda ya zama daidai da kisan kare dangin da ya taba faruwa a Rwanda.

Babban mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Laraba, 25 ga watan Agusta ta shafinsa na Facebook.

Shehu ya ce kamar yadda ya faru a Rwanda inda shugabannin Hutu na wancan lokacin suka tunzura ‘yan kasarsu a kan junansu, inda suka ce akwai “boyayyar manufar Tutsi” kan Hutu, Ortom ma haka ya ce akwai “boyayyar manufar Fulani” kan sauran kabilun jaharsa da kasar.

“Gwamna Samuel Ortom na da karancin sanin ka’idojin siyasa. Za mu iya ganin haka daga yadda ya canza jam’iyyarsa sau biyar a lokacin da bai yi fice ba.

“Duk lokacin da ya ji guguwar canji na kadawa ta wata hanya, sai ya bi ta.

“Abin takaicin shine, ga mutanen kirki na jahar Benue, shine mawuyaciyar alkiblar da yake kadasu a yau itace na bangaranci da kabilanci.

“A wani yunkuri na hakaka siyasarsa, Ortom na daukar hanya mafi arha kuma mafi kaskanci ta hanyar wasa da kabilanci – kuma yin hakan da gangan ya jawo mutuwar ‘yan Najeriya marasa laifi ta hanyar tunzura manoma akan makiyaya, da Kiristoci akan Musulmai.

Mutanen Benue basu cancanci irin wannan gwamnan ba

A cewar Garba Shehu, al’ummar jahar Benue bai kamata ace suna da irin wannan shugaba ba, kuma yana addu’ar Allah ya kawo zabe na gaba su hambarar da gwamnatinsa.

A kalamansa, Shehu yace:

“Wadannan ba ayyukan mutum bane da ya kamata a amince da shi wajen gudanar da ayyukan gwamnati ko rike mukamin gwamnati.

“A ce gwamnan wata babbar jaha a Najeriya ya nuna kiyayya ta kabilanci a siyasance, tabo ne ga kasarmu. Mutanen kirki, kuma masu adalci a jahar Benue sun cancanci fiye da wannan, kuma muna dokin zuwan zabe lokacin da za su sami damar maido da martabar ta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here