Arewa: Bincike ya Nuna Akwai Sansanin ‘Yan Ta’adda 120 da Bindigogi Kirar AK-47 60
Wani malamin jami’a ya gudanar bincike, inda ya gano wasu abubuwan ban tsoro game da ‘yan bindiga.
A cewarsa, ya gano a kalla akwai bindigogi AK-47 60,000 a sansanonin ‘yan bindiga sama da 120 a yankin Arewa maso yamma.
Ya kuma ba da wasu alkaluman kashe-kashe da barnar ‘yan bindiga a dukkan yankunan na Arewa maso yamma.
Sokoto – A wani rahoto da muka sami, an ce akwai akalla sansanonin ‘yan ta’adda 120 da ke da mallakin bindigogi kirar AK-47 guda dubu 60, a jahohin Arewacin kasar nan shida, Tribune Nigeria ta rawaito.
jahohin sune Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna, Kebbi da Neja kuma kowanne daga cikin kungiyoyin ta’addancin 120 sun mallaki bindigogi AK-47 sama da 500.
Wadannan bayanan suna kunshe ne cikin binciken shekaru goma da wani babban malami a Sashen Tarihi na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Dakta Murtala A. Rufa’i ya gudanar.
Malamin, wanda ya bi diddigin ayyukan ta’addanci daga shekarar 2011, ya kuma ce sama da rayuka 12,000 ne suka salwanta a ta’addanci a jahar Zamfara kadai.
Read Also:
Ya kuma bayyana cewa kimanin dabbobi 250,000 aka sace, yayin da aka lalata kauyuka 120 sannan sama da mazauna kauyuka 50,000 da ‘yan ta’adda suka raba da muhallansu a cikin wannan lokaci da ya yi nazari.
Ya yi wannan jawabi ne a wata laccar jami’ar a zaman wani bangare na shirye-shiryen karawa juna sani kan fashi da makami a shiyyar Arewa maso Yamma.
Yayin da yake gabatar da takardar binciken mai taken, “Ni Dan Bindiga ne:
Shekaru Goma na Bincike a Maboyar ‘Yan Ta’adda a Zamfara”, Rufa’i ya ce ya yi mu’amala daya bayan daya da wasu shugabannin kungiyoyin ta’addanci.
A cewarsa, wadannan gungun ‘yan bindiga da gaske suna kisan gilla kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, satar shanu, garkuwa da mutane, cin zarafin mata da sauran laifukan da suka danganci take hakkin dan adam.
A cewarsa:
“Da farko, sun zauna a cikin dazuzzuka da duwatsu inda suke kaddamar da ta’addanci a yankunan karkara da birane na jahohi. Amma wasu daga cikin ‘yan bindigar sun zama masu karfin hali har suke iya farautar su daga garuruwan su.”
Ya kara da cewa:
“Sansanoni masu karfi da kungiyoyi kamar wanda Dan-Karami na Zurmi ke jagoranta, Alhaji Auta na Birnin Magaji, Halilu na Chafe, Turji na Isa da Dogo Gide na Birnin Gwari suna da karfin kudi da hadin gwiwa don siyan adadi mai yawa. na makamai.”
Rufa’i ya bayyana a cikin bincikensa na karawa juna sani, inda ya yi cikakken bayani kan yadda ‘yan bindigan suke sake shiga cikin kungiyoyin ta’addanci.