Najeriya: Kasar Saudiyya ta Nuna Alhinin Kisan Manoma
Kasar Saudiyya ta bayyana alhininta a kan kisan manoman jihar Borno da ake zargin ‘yan Boko Haram sun yi.
Saudiyya ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda al’amarin ya shafa da gwamnatin Najeriya gaba daya.
Ta kuma yi fatan Ubangiji ya nuna ranar da za a kawo karshen ta’addanci da kashe-kashe a Najeriya.
Read Also:
Saudiyya ta nuna alhininta a kan kisan manoman shinkafa da ake zargin ‘yan Boko Haram sun yi a Borno.
Saudiyya ta wallafa wannan sakon a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta nuna alhininta a kan yadda maharan suke kai wa fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba fargaba.
Kamar yadda ta wallafa, “Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe, da mutanen jihar, gwamnati da al’ummar Najeriya gaba daya.”
Kasar Bahrain ta mika kwatankwacin ta’aziyyar nan ga Najeriya, inda tace tana fatan ganin karshen ta’addanci a Najeriya nan kusa.