Kasar Saudiyya ta Bude Iyakokin Kasar

 

Saudiyya ta sake bude iyakokin kasarta ga masu shigowa daga kasashen duniya.

Kasar ta bayyana cewa wasu maso shigowa sai sun debe kwanaki hudu a killace kafin shiga kasar.

Kasar ta bayyana samun saukin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar.

Saudiyya a ranar Lahadi ta sanar da sake bude kan iyakoki da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa bayan dakatarwar da aka yi ta makwanni biyu da nufin dakile yaduwar wata sabuwar cutar ta Covid-19.

Gwamnatin ta ba da umarnin a dauke “matakan kariya da suka shafi yaduwar wani sabon nau’in kwayar cutar corona,” in ji ma’aikatar cikin gidan, a cewar kamfanin dillancin labarai na Saudi Arabia.

Saudi Arabiya ta bayyana samun sama da mutane 363,000 da suka kamu da cutar, ciki har da sama da mutane 6,200 da suka mutu – mafi girma a tsakanin kasashen larabawan Tekun Fasha – amma kuma ta bayar da rahoton yawan samun sauki.

Riyadh ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa da kuma isa ta mashigar kasa da mashigai a ranar 21 ga Disamba.

Sauran kasashen yankin Gulf, Oman da Kuwait, wadanda suka dauki irin wannan matakin, suma sun dauke su a kwanakin baya.

Amma matafiyan da suka dawo daga Biritaniya, Afirka ta Kudu ko “duk wata ƙasa da sabon nau’in kwayar cutar ta coronavirus ke yaɗuwa” za su fuskanci ƙarin takunkumi, in ji sanarwar.

Baƙi da ke zuwa daga waɗannan ƙasashen dole ne su kwashe kwanaki 14 a wata ƙasa kafin su shiga Saudi Arabiya, kuma su nuna gwajin cewa ba sa dauke da cutar.

‘Yan kasar ta Saudiyya da suka dawo daga wadannan kasashen za su iya shiga kai tsaye – amma dole ne su kwashe makonni biyu a keɓe lokacin isowa, kuma za a yi musu gwaji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here