Saudiyya ta yi wa ɗaliban Najeriya Bushara

Daliban Najeriya 424 zasu amfana da kyautar guraben karatu a jami’o’in Saudiyya daban-daban.

Kasar Benin ita ma zata samu makamancin gurbin karatun guda 150 kyauta daga Saudiyya.

Ofishin jakadancin Saudiyya ya yaba da irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Najeriya da sauran kasashen Afirka.

Masarautar Saudiyya ta ce zata bada guraben karatu kyauta ga daliban Najeriya 424 don yin karatu a bangarori daban daban a jami’o’in Saudiyya.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Kasar ya fitar a Abuja, ranar Litinin, ta ce guraben na cikin 6,597 da Saudiyya ke bawa daliban Afirka.

Sanarwar ta kuma ce, ana bawa daliban Jamhuriyyar Benin guraben karatu kyauta 150 duk shekara.

“Domin sanin hanyar da za a bi da kuma abubuwan da ake bukata don neman gurbin kyautar karatun, dalibai su nemi bayanai daga ma’aikatar harkokin kasashen waje da kuma ma’aikatun ilimin kasashen su.

Za kuma a iya samun bayani daga ofishin jakadancin Kasar Saudiyya. “Ofishin jakadancin ya kuma yaba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Saudiyya da Najeriya da kuma sauran kasashen Afirka,” a wani bangare na sanarwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here