Kasar Saudiyya ta Sanar da Mafi Karancin Shekarun Aure
Mahukunta a kasar Saudiyya sun tsayar da shekaru goma sha takwas a matsayin mafi karacin shekarun aure.
A wata takardar mai dauke da sa hannun ministan shari’a kuma shugaban kotunan Saudi, an umarci kotunan kasar su fara aiki da dokar.
An dade ana muhawara a kan mafi karancin shekarun aure ko aurar da ‘yammata kafin kasar Saudiyya ta dauki wannan mataki.
Read Also:
Ma’aikatar Shari’a ta ƙasar Saudiyya ta haramta aure ko aurar da ƴammata ‘yan ƙasa da shekara goma sha takwas da haihuwa.
Kazalika, gwamnatin kasar ta kuma saka dokar shekara 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da za’a yi aure.
Ministan Shari’a kuma Shugaban kotunan ƙasar, Sheik Walid Al-Samaani, shine ya bada sanarwar dokar ga duk kotunan da ke faɗin ƙasar Saudiyya.
Acewar Jaridar Premium Times, auren ƙananan yara mata a saudiyya abune da aka saba.
A cikin yara mata bakwai, ɗaya daga cikinsu ta na aure kafin cika shekaru 18.