Sauya Takardun Naira ya Taimaka Wajen Rage Aikata Manyan Laifukan Garkuwa – Emefiele

 

Gwamnan CBN ya ce a tunaninsa sauya takardun naira ya taimaka wajen rage aikata manyan laifukan garkuwa.

Godwin Emefiele yace mai yuwawa sabon tsarin ya rage wa yan ta’adda karfin karɓan kudin fansa saboda ba’a amsar tsoffi.

Yace babban bankin ƙasa bai manta da mutanen karkara da masu karamin karfi kuma zai neme su ko da bayan karewar wa’adi.

Abuja – Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, yace sabbin takardun kuɗin da aka sauya sun rage yawan garkuwa da mutane da karɓan kuɗin fansa.

Gwamnan ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake jawabi bayan taron kwamitin tsara takardun naira na bankim CBN a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Channels tv tace a yayin wannan jawabi ne Emefiele ya jaddada cewa ba gudu ba ja baya game da karewar wa’adin tsoffin takardun N200, N500 da N1,000 ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

“Magana ta gaskiya, a ɗan wannan lokacin, zata iya yuwuwa ba haka bane amma a tunani na garkuwa da mutane da kuma neman kudin fansa sun ɗan ragu ta wani fannin. Jami’an tsaro sun kara zage dantse.”

“Ina ganin (sauya takardun naira) ya sa mutanen nan sun ja baya saboda sun san idan suka karbi tsaffin kuɗi ba zasu amfane su ba. Tunani na zai iya zama haka ne zata iya yuwuwa kuma ba haka bane.”

– Godwin Emefiele.

Gwamnan ya kara da bayanin cewa CBN na sane da mutane masu karamin karfi da yan kauye kuma bankin zai je har inda suke don tabbatar da sun samu sabbin takardun.

Bayan haka, Gwamna Emefiele ya sanar da ƙara kuɗin riba MPR daga kashi 16.5% zuwa kaso 17.5% da nufin dakile hauhawar farashi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar Godwin Emefiele ba bu ɗan Najeriya fa aka ba shi lasisin gima wurin ajiyar kuɗaɗe a cikin gidansa.

 

nigerian news today headlines

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here