Buhari Zai Ziyarci Kano Don Kaddamar da Muhimman Ayyukan da Ganduje Yayi

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Kano a mako mai zuwa na tsawon kwanaki biyu kamar yadda kwamshinan yada labaran jihar ya sanar.

Buhari wanda zai je Kano a ranar Litinin 30 zuwa 31 ga watan Janairu, zai kaddamar da muhimman ayyukan da Gwamna Ganduje yayi a jihar.

Zai kaddamar da wutar lantarki mai zaman kanta ta jihar, aikin Dam don Tiga, cibiyar koyar da sana’a ta Dangote da sauransu duk a cikin kwanakin biyu.

Kano – Shugaba Muhammad Buhari zai kaddamar da aikin wutar lantarki mai zaman kanta ta jihar Kano a ziyarar kwana biyu da zai kai jihar daga 30 zuwa 31 ga watan Janairun 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Kwamishinan yada labari na jihar kuma kakakin gwamnan, Muhammad Garba, ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai kan kokarin kwamitin wurin tabbatar da nasarar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Hakazalika, Garba ya bayyana cewa a yayin ziyarar kwanaki biyun da zai kai, zai kaddamar da ayyuka a cibiyar koyar da ayyukan dogara da kai ta Dangote, Dala Inland Port, rukunin gidajen malamai na karamar hukumar Ungogo, aikin wutar lantarki mai zaman kansa, Tiga Dam da gadar Muhammadu Buhari.

Megawatts 10 na wutar lantarkin za su dinga ba wa fitillun kan tituna, masana’antu, ayyukan wutar lantarki da sauran muhimman bangarori.

A yayin jawabi kan zaben, Garba ya bayyana tabbacinsa da kwarin guiwa kan cewa ‘dan takarar gwamnan jihar na APC ne zai lashe zaben.

A yayin sharhi kan zaben da ba a kammala ba, Garba yace lamari ne da ya shafi kundin tsarin mulki inda ya kara da cewa za a kare faruwar hakan a 2023 kamar yadda yace APC za ta kare kuri’unta a zabukan.

nigerian newspapers read them online

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here