Ganduje ya Biya Bashin N18bn da Kwankwaso ya Bari na Kudin Makarantar Dalibai

 

Ganduje ya biyan Naira bilyan 18 cikin bashin kudin makarantar daliban jihar masu karatu a kasar waje.

Gwamnatin yace tace Kwankwaso ya danawa Ganduje tarko saboda tarin basussukan ya bar masa.

Kwamishanan labaran jihar yace idan mataimakin gwamnan Kano ya zama gwamna zai gyara tsarin.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya biya bashin kudin makarantun daliban jihar da gwamnan maigidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso ta tura kasashen waje.

Kwamishanan labaran jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana haka a jawabin da ya fitar jiya, rahoton TheNation.

Ya bayyana cewa kudin N18bn, bashi ne na kudin makarantan dalibai yan asalin jihar Kano da ke karatu a kasashen waje.

Ya ce mafi akasarin daliban na karatu ne a kasar Faransa, Cyprus, da Masar.

Garba ya ce gwamnatin Kwankwaso ce ta fara wannan tsari amma ta ki biyan dalibai kudin.

A cewarsa:

“Lokacin da muka hau mulki a 2015, mun samu dimbin bashin kudin daukar nauyin karatun dalibai da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta bari kuma wannan abu ya bamu matsala.”

“Amma mun biya kimanin N18bn kawo yanzu.” Garba ya caccaki gwamnatin Kwankwaso bisa yadda ta tura dalibai kasashen waje karantar ilmin da akwai su a Najeriya kuma a farashi mai arha, riwayar Tribune.

Yace gwamnatin Ganduje bata ki a tura dalibai kasar waje karantar ilmin da babu a Najeriya ba, amma rashin tunani ne a tura dalibai karantar ilmin tarihi a kasar waje.

Yace gwamnatin Kwankwaso bata bi tsarin da ya kamata wajen tsara shirin ba kuma akwai cakwakiya ciki. A cewarsa, idan Gawuna ya samu nasarar danewa mulki, zasu gyara wannan tsari.

Yace:

“Idan aka zabi Gawuna matsayin gwamnan Kano, ko shakka babu zai yi dubi cikin shirin kuma ya gyara. Daliban da zasu amfani karatukan da zasu amfani jihar kadai zasu yi.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here