Shirinta na nukiliya: Mun Shirya Amfani da Wasu Hanyoyi na Daban na Hukunta Iran – Amurka
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce sun shirya amfani da wasu hanyoyi na daban na hukunta Iran matsawar ta ci gaba da nuna tirjiya kan batun shirinta na nukiliya.
A wani zama da takwarorinsa na Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa, Mr Blinken ya gargadi gwamnati a Tehran cewa lokaci na kure mata na ta cika alkawuran da ta dauka game da yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da ita a 2015.
Tun bayan hawan sabon Shugaba Ebrahim Raisi a watan Agusta, har yanzu Iran bata waiwayi batun nukiliyar ba.
Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a lokacin tsohon Shugaba Donald Trump, wanda ya fusata gwamnati a Tehran ta cigaba da tara sinadarin uranium wanda ya saba alkawarin da aka yi da ita a baya.