Mun Shirya wa Zaben Anambra – Janar Usman Alkali Baba
Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya ce rundunarsa ta shirya tsaf don ganin cewa an gudanar da zabe cikin lumana a jahar Anambra da ke Kudancin kasar.
IGP Usman Alkali Baba ya bada tabbacin a wani zama da yayi da wasu kwamandodin rundunar yau a Abuja, inda ya ce ba za su yi kasa a gwuiwa ba wurin fatattakar bata gari daga nan har bayan zaben na 6 ga watan Nuwamba.
Yanzu haka jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da takun saka da masu tada kayar baya a yankin Kudu maso Gabas, da suka hada da kungiyar yan awaren Biafra ta IPOB da ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya a yankin.
Ko a jiya Talata an zargi IPOB da kai wa tawagar gwamnan jahar Anambra hari.
Bugu da kari Sifetan yan sandan ya bai wa hukumar zaben Najeriya wato INEC tabbacin bai wa ma’aikatanta da kuma kayan aikinta kariya a lokacin zaben.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here