Igboho na Fama da Ciwon Koda a Gidan Yarin Benin – Lauya
Lauyan mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Najeriya Sunday Igboho ya ce gwaji ya nuna cewa akwai alamun yana dauke da ciwon koda ko na huhu.
A hira da sashen Yarbanci na BBC Barista Yomi Aliyyu ya ce wanda yake karewar ya kamu da cutar ne yayin da ya ke tsare a Jamhuriyar Benin.
A cewarsa har ma an garzaya da shi asibiti bayan da rashin lafiyarsa ta yi tsanani.
Jami’an tsaro a Najeriya sun kai samame a gidan Sunday Igboho da ke garin Ibadan na jahar Oyo da ke Kudanci a ranar 1 ga watan Yulin 2021, inda suka kama mutun 12.
Sai dai a ranar 16 ga watan Yuli ne aka kama Mr Igboho a Coutonou da ke Jamhuriyar Benin ind ayanzu haka ake tsare dashi.
Rahotanni sun nuna cewa yana kokarin tsallakawa Jamus ne a lokacin.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here