APGA Zuwa APC: Mataimakin gwamnan jahar Anambra ya Sauya Sheka
Mataimakin gwamnan jahar Anambra Nkem Okeke ya sauya sheka daga jam’iyar APGA zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an gabatar da Mr Okeke ga Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a yau Laraba, ta hanyar Shugaban jam’iyar na riko kuma gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni da kuma gwamna Hope Uzodinma na jahar Imo.
Sauya shekar mataimakin gwamnan na zuwa yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jahar ta Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here