Shugaban Kasa 2023: Wasu ‘Yan Arewa Sun Zabi Gwanin Su

Wasu ‘Ya ‘yan APC suna so mulkin Najeriya ya koma Kudu a zaben 2023.

Kungiyar tana ganin abin da ya dace shi ne a ba Arewa shugaban Jam’iyya.

Bashir Yusuf ya ce Abdulaziz Yari ne ya kamata a bar wa rikon Jam’iyyar.

Wata kungiya ta ‘yan siyasar da suka nemi kujeru a jam’iyyar APC a 2018, suna goyon bayan shugaban kasa ya fito daga kudancin Najeriya.

Jaridar Guardian ta ce wadannan ‘ya ‘yan na APC suna son ganin magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin kudu.

Bashir Muhammed Yusuf a wata hira da ya yi da ‘yan jarida da yawun bakin kungiyar tasu ya bayyana wannan jiya a birnin tarayya Abuja.

Alhaji Bashir Muhammed Yusuf ya ke cewa tun da yanzu mulki na hannun ‘dan Arewa, ya kamata a zabe mai zuwa, a mika takara zuwa Kudu.

Yace: “Wannan shi ne abin da muke so, kuma shi ne ya fi dacewa da kasar nan. Hakazalika, shugaban jam’iyya zai dawo Arewa, sai a juya kujerun.”

A ra’ayin Bashir Muhammed Yusuf, babu wanda ya dace ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa illa tsohon gwamna Alhaji Abdulaziz Yari.

Kungiyar tana ganin cewa idan APC tana son samun nasara a zaben 2023, to Abdulaziz Yari ya kamata ya maye gurbin da Adams Oshiomhole ya bari.

Abdulaziz Yari ya yi gwamna har sau biyu a jihar Zamfara, sannan ya rike shugaban kungiyyar gwamnonin jam’iyyar APC a lokacin da yake ofis.

Kungiyar ta ce APC tana bukatar cikakken ‘dan jam’iyya, wanda ya san harkar siyasa, sannan ya fahimci abin da shugabanci da rike mukami ya kunsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here