‘Yan Bindiga Sun Kashe Wasu a Kaduna

 

Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da mutuwar wasu mutum biyu.

Aruwan ya ce ‘yan bindigan da jami’an tsaro suka fatattaka ne yayin da suka yi yunkurin kaiwa matafiya hari a hanyar Kaduna zuwa Abuja suka kai harin.

Baya ga mutum biyu da ‘yan bindigan suka kashe sun kuma raunta wasu mutane biyu a garin na Maigiginya ‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu a garin Maigiginya da ke karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

An kai harin ne misalin karfe uku na daren ranar Talata kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakayya sunansa sabioda tsaro ya ce ‘yan bindigan sun raunta mutane biyu kafin su tsere.

Wadanda aka kashe sunansu Nasiru Yahaya da Isah Bature. Wadanda aka raunta kuma sune Magaji Goma da Zurkhalaini Alhassan.

“Yan bindigan sun kuma sace kayayyakin abinci. Kwamishinan Tsaron cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da afkuwar harin da kashe mutanen biyu.

Acewarsa, ‘yan bindigan da suka kai hari a kauyen suna hanyarsu na tserewa bayan jami’an tsaro sun dakile harin da suka yi yunkurin kaiwa a babban titin Kaduna zuwa Abuja a daren ranar Litinin.

“An sanar da gwamnatin Jihar cewa dakarun atisayen Operation Thunder Strike a daren ranar Litinin sun yi nasarar dakile harin ‘yan bindiga a babban titin Kaduna zuwa Zaria.

“Yan bindigan sun bullo a kusa da bututun man fetur da ke unguwar Kakau da nufin kai wa matfiya hari inda dakarun sojoji suka tare su suka fattatake su,” in ji Aruwan.

Aruwan ya tabbatar da rasuwar mutane biyun a garin Maigiginya da ke karamar hukumar Igabi da suka sauran mutum biyu da suka jikkata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here