Gwamna Zulum ya Bayyana Cewa Siyasantar da Harkokin Tsaro ne ke Ta’azzara Al’amura a Najeriya
Gwamnan jahar Borno da ke arewacin Najeriya Babagana Umara Zulum ya yi zargin cewa siyasa da aka sanya wajen daukar jami’an tsaro a kasar ita ke kara dagula al’amura, abin da ya jefa harkokin tsaron kasar a hannun masu neman aiki.
Zulum ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da yake gabatar da wata makala Kuru da ke jahar Plateau.
Ya ce:
“Ya ce babbar matsalar yadda ake daukar aiki ne. Mafi yawan wadanda ake dauka aiki a rundunar sojojin Najeriya da ta ‘yan sanda da suran hukumomin tsaro masu neman aiki ne kawai. Da yawa suna aikin ne domin basu da abin yi.
Ya ce:
Read Also:

“Wadanda aka dauka shekara 20 baya sun yi abin da ya kamata saboda suna da sha’awar aikin, amma na yanzu neman aikin kawai suke yi, babu sadaukarwa babu nuna damuwa.
“A yanzu ko wanne gwamna da minista da sauran masu madafan iko na da gurbi da ake basu na suka wo wanda suke so a dauka aiki.
Babu wanda zai yi musu jarrabawar ko suna da sha’awar aiki ko kuma a a. An siyasantar da daukar jami’an tsaro aiki.

Zulum ya kara da cewa matukar ba muyi abin da ya dace ba, babu abin da zai tafi dai-dai.