Corona: Karin mutane 437 sun kamu da Cutar a Najeriya

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 437 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jahar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 126 da suka kamu da cutar a jahar yayin da jahar Ribas aka samu mutum 76 da suka kamu da cutar sai kuma jahar Kwara da aka samu mutum 44.

Ga jerin jahohin da aka samu bullar cutar ranar Litinin:

Lagos-126

Rivers-76

Kwara-44

FCT-37

Edo-32

Kaduna-30

Anambra-22

Delta-22

Osun-12

Benue-7

Abia-6

Nasarawa-6

Kano-5

Ekiti-3

Plateau -3

Bayelsa-2

Ogun-2

Oyo-2

A jumullance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 205,484 sai dai 193,482 sun warke.

Akwai kuma mutum 2,701 da suka mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here