Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram Kan Turakun Wutar Lantarki a Yobe

 

Lokaci kaɗan bayan gyara wutar yankin Arewa maso Gabas, ’yan ta’addan Boko Haram sun yi kokarin kai hari tare da sake lalata wutar.

Sai dai dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile harin da maharan suka shirya kan manyan turakun wutar lantarki a yankin mai fama da rikici.

Lamarin ya faru ne a kauyen Kesesa da ke kusa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe a ranar Asabar, 6 ga watan Yulin 2024.

Dakarun dai sojojin sun yi nasarar dakile harin ne tare da taimakon mafarauta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata rahoto da Zagazola Makama, ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ya fitar a ranar Lahadi.

To sai dai rahoton ya ce daga bisani dakarun sun fatattaki ‘yan ta’addan tare da raunata wasu da dama daga cikinsu.

Yadda suka shirya kai harin

Zagazola ya ce, “Dakarun sojoji sun dakile harin Boko Haram kan manya-manyan turakun da ke dauke da wutar lantarki a Kasesa da ke bayan garin Damaturu.

“Yan ta’addan sun yi kokarin lalata turakun wutar kafin dakarun da taimakon mafarauta su sami nasarar dakile shirinsu.

“Bayan kai ruwa rana da dakaraun, maharan sun gudu sun bar motarsu da fasassun tayoyi biyu har ma da jini a jikinta da ke nuna sun samu raunuka,” in ji Zagazola Makama.

Rahoton ya ce bayan bincike, an gano abubuwan fashewa a motar wacce aka samu wasu katuna mallakin wani mai suna Emmanuel Adamu a cikinta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here