ENDSARS:Sojojin Najeriya sun Musanta Harbin Masu Zanga-Zangar a Legas

Rundunar sojojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa dakarunta sun buɗe wuta ga masu zanga-zangar #ENDSARS a Lekki da ke Legas.

Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da cewa aƙalla mutum 30 ne suka samu rauni a yammacin Talata bayan tarzomar da ta shi a wurin.

Ƙungiyar ƙare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana cewa an kashe masu zanga-zanga da dama yayin harbin da aka yi a Lekki.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun ta yaɗa bidiyo inda ake jin harbe-harben bindiga a tsawon daren.

Wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa ya ƙirga gawarwaki har 20 da kuma gwamman mutanen da suka ji rauni.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here