Sojojin Najeriya Sun Kama Babban Kwamandan Boko Haram, Yawi Modu
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kama wani babban kwamandan Boko Haram da ake kira Yawi Modu, wanda a kwanan nan ta ce tana nema ruwa a jallo.
Read Also:
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a Abuja jaridar Premium times ta wallafa , Kakakinta Onyema Nwachukwu ya ce rundunar ta kai wani samame ne wani wurin hada abubuwan fashewa da ke jahohin Yobe da Borno.
Rundunar ta ayyana wasu mutane sama da 100 shekara biyar baya da take nema ruwa a jallo.
Kuma ta wallafa sunayensu tare da makalesu a bainar jama’a.
Wannan na zuwa ne dai lokacin da wasu membobin kungiyar ke ci gaba da tuba tare da mika wuya ga jami’an tsaro tare da iyalansu.
Sama da shekara 10 Boko Haram da ISWAP ke gudanar da ayyukansu na tada kayar baya a yankin arewa maso gabas da kuma yankin lafkin Chadi.