‘Yan Fashin Dajin Zamfara Sun Fara Bukatar Kayan Abinci a Madadin Kudin Fansa

 

‘Yan fashin daji a jahohin arewa maso yamma sun fara shiga mawuyacin hali tun bayan rufe kasuwanni.

Sun fara bukatar buhunan shinkafa, kwalayen taliya da na ruwan lemo a madadin kudin fansar wadanda suka sace.

Wasu mazauna yankin sun sanar da yadda yunwa ta gigita ‘yan bindigan har suka karba mudu goma na shinkafa a matsayin fansa.

Zamfara – Rufe kasuwanni masu yawa a fadin jahohin arewa maso yamma na Najeriya ya kasance babban kalubale ga ‘yan fashin daji.

Daily Trust ta rawaito cewa, a kalla gwamnonin yankin hudu ne suka umarci rufe kasuwannin jahohinsu a matsayin hanyar dakile ta’addanci.

Kwanaki kadan bayan rufe kasuwannin a wasu kayukan Sokoto, ‘yan fashin daji sun fara bukatar kayan abinci a matsayin fansar wadanda ke hannunsu.

Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya bukaci a rufa sunan shi, ya sanar da Daily Trust yadda aka sako wata diyar makwabtansu bayan sun bada kayan abinci.

“Sun sace diyar wani mutum a kauyenmu kuma ya kasa hada kudi, sai suka ce ya kai mudu goma na shinkafa a matsayin fansar diyarsa. Haka kuwa a ka yi.”

Wani mazaunin Sokoto ya sanar da Daily Trust yadda ‘yan bindiga suka bukaci kayan abinci da abubuwan sha domin sakin direban da suka sace.

Da farko sun bukaci kudin fansa har N15 miliyan, amma daga baya sun amince za su karba N600,000.

“Sun bukaci a yi amfani da kudin wurin siyan buhunan shinkafa, katon din abin sha, kwalin taliya, sigari da sauransu. Har yanzu dai ana tattaro kudin,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here