Idris Jere ya Zama Sabon Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice

 

Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 36 yana aiki.

Zuwa lokacin da za a nada sabon CG, Idris Isah Jere, Mataimakin Kwanturola Janar ya karbi ragamar aiki.

A yayin bikin barinsa mulki a ranar Juma’a, tsohon CG ya yi alfahari da cewa ya bar NIS fiye da yadda ya same ta.

FCT, Abuja – Idris Isah Jere, Mataimakin Kwanturola Janar mai kula da Kudi, ya zama  mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS).

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Jere ya karbi mukamin mukaddashin hukumar daga Muhammad Babandede har zuwa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai nada Babban Kwanturola Janar.

Legit.ng ta tattaro cewa Babandede ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 36 yana aiki.

Da yake magana a taron saukarsa daga kujerar shugabanci wanda aka shirya don girmama shi a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba, Babandede ya ce ya bar NIS fiye da yadda ya same ta, jaridar The Cable ta rawaito.

CG mai ritaya ya yi alkawarin cewa zai kasance a shirye a koyaushe don taimakawa a duk lokacin da aka kira shi.

Babandede ya kwashe shekaru biyar a matsayin Kwanturola Janar na NIS.

Yan Najeriya sun jinjinawa Babandede

Ameenour Abour Ner’Arlie Kaurah yayi sharhi akan Facebook:

“Bankwana ga sarkin gyara, sarkin ayyuka, CGIS na zamani.”

Salisu Muhammad Bello ya ce:

“Wannan babban jami’in tsaro ne mai kwazo da mutunci. Ina yi maka fatan alkairi kwanturolar hukumar kula da shige da fice.”

Aliyu Bello ya ce:

“Ya kamata Buhari ya samu wanda zai iya kula da iyakokinmu don gujewa shigowa da makamai masu sauki …. Ina taya ka murna Babandede kan namijin kokarin da kayi!”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here