Wadanda Ake Ganin Zasu Iya Maye Gurbin Tsohon Ministan Noma, Sabo Nanono

 

Hasashe sun nuna cewa mutum daya daga cikin Nasiru Baballe Ila, Alhaji Akibu Ibrahim Bello, Ismaeel Buba Ahmed da Suleiman AbdulRahman na iya zama sabon ministan Shugaba Buhari.

Hakan ya biyo bayan sallamar ministoci biyu na noma da lantarki da shugaban kasar yayi.

Sai dai kuma babu wani tabbaci a hukumance da ke nuna haka, domin duk shawara ce ta wasu jiga-jigan APC da ke ganin sun cancanta.

Abuja – Biyo bayan korar Sabo Nanono daga mukamin ministan aikin gona, wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna mutane hudu da Shugaba Muhammadu Buhari ka iya nadawa don maye gurbinsa.

Nanono wanda aka kora a ranar Laraba, 1 ga Satumba ya fito ne daga jahar Kano. An tattaro cewa ‘yan uwansa sun fara zawarcin gaske don ganin wanda ya maye gurbin ya fito daga jahar.

Ga jerin mutum hudu da ka iya maye gurbin Nanono, a cewar rahoton:

1. Suleiman AbdulRahman (wanda aka fi sani da Kawu Sumaila), tsohon babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan al’amuran majalisar dokoki.

2. Ismaeel Buba Ahmed, Babban Mataimaki na Musamman ga shugaba Buhari kan Shirin tallafawa jama’a na kasa.

3. Nasiru Baballe Ila, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Tarauni a majalisar dokokin kasar.

4. Alhaji Akibu Ibrahim Bello, tsohon shugaban karamar hukumar Nassarawa.

Duk da haka Daily Trust ta lura cewa babu wata kungiya a Kano da ta yi kira ga shugaban kasa a hukumance kan ya nada wani daga cikin mutanen da aka lissafa.

An dai jero su ne kawai yayin da wasu jiga -jigan ‘yan jam’iyyar APC mai mulki suka ba da shawarar a matsayin wadanda za su iya maye gurbin.

A cewar rahoton, ana kara samun karin haske kan hasashen wanda ka iya maye gurbin Nanono.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here