‘Yan Siyasa Sun Kashe ‘Yan Najeriya da Basu ji ba Basu Gani ba fiye da ‘Yan Fashin – Sheikh Gumi

 

Shahararren malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi karin haske kan tattaunawar da ya yi da ‘yan fashin.

Gumi ya ce wasu fitattun ‘yan Najeriya na yin zagon kasa a kokarin da yake yi na tattaunawa da ‘yan bindigar.

Malamin, ya lura cewa wasu ‘yan siyasa sun kashe ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba fiye da ‘yan fashin.

Kaduna – Sheikh Ahmed Gumi, fitaccen malamin addinin Islama kuma mai wa’azin addini, ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa sun fi ‘yan fashi muni saboda illolin almubazarancin da suka yi da albarkatun kasar ya kashe ‘yan Naeriya fiye da’ yan fashi.

Legit.ng ta rawaito cewa Gumi ya bayyana haka ne a wani sharhi da yayi a shafinsa na Facebook mai taken, ‘Yaki bai taba zama mafita a ko ina ba, a kowane lokaci.’

Ya ce wasu ‘yan Najeriya sun mutu sakamakon cutar kwalara saboda rashin tsaftataccen ruwan sha.

Gumi ya ce:

“Wasu daga cikin ‘yan siyasa, wadanda nake kallo a matsayin ‘yan fashin birni, saboda illata mana albarkatunmu da suka yi da rashin ba abubuwa muhimmanci, suna haifar da mutuwar mutane da nakasa su fiye da ‘yan fashi.”

Gumi ya ce wasu masu fada a ji a kasar suna yiwa aikinsa zagon kasa.

Malamin ya ci gaba da bayyana cewa wasu mutane marasa son zaman lafiya sun ce zaman lafiya da tattaunawa da makiyaya da ‘yan fashi bai cimma nasara ba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here