Jahar Eikiti Zata Nada Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmed Lawan da Fitattun ‘Yan Najeriya 6 Saurautar Iyin-Ekiti

 

Za a nadawa Ahmad Lawan sarautar Iyin-Ekiti, a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun.

An bayar da rahoton cewa za a nada masa masarautar ne bisa ga irin gudummuwar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa gaba ɗaya.

Sauran wadanda kuma za a karrama su ne: Manjo Janar Bamidele Olawumi da matarsa, Ba’isra’ile, Him Hille da matarsa, da sauransu.

Ekiti – Za a nadawa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da wasu fitattun ‘yan Najeriya shida sarautar Iyin-Ekiti, a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun ta jahar Ekiti.

Sauran su ne tsohon Darakta Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Manjo Janar Bamidele Olawumi da matarsa, Ba’isra’ile, Him Hille da matarsa, Mista Ayodeji Adeosun da Mrs Veronica Ndanusa.

Sarkin Iyin-Ekiti, Oba Adeola Ajakaiye; Oluyin na Iyin-Ekiti, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a Iyin-Ekiti, jaridar PM News ta rawaito.

Rahoton ya kuma kawo cewa za a shafe mako guda don gudanar da taron cika shekara guda da hawan sarkin kan karagar mulki daga ranar Litinin.

Ajakaiye ya ce za a yi masu nadin sarautar ne don karrama gudummawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma da kasa baki daya.

A cewar basaraken, sauran ayyukan da aka shirya don tunawa da ranar sun hada da, kaddamar da Naira miliyan 500 na asusun raya masarauta da duba lafiya.

Sauran ayyukan sun hada da warkar da mutane da yi masu tiyata da gasar kwallon kafa, da sauransu.

Ya yi kira ga ‘ya’yan garin maza da mata, na gida da na kasashen waje, da su rika bayar da gudunmawarsu a ko da yaushe don ci gaban al’umma.

Sakataren masarautar Oluyin, Cif Opeyemi Arije, ya lura cewa garin ya sami gagarumin zaman lafiya da ci gaba a cikin shekara guda na mulkin sabon sarkin.

Arije, wanda ya ninka a matsayin Sakataren Kwamitin Shirye -shirye na Karamar Hukumar, ya ce al’umman suna fuskantar wani sabon ci gaba.

“Sarkin mu ya yi gyaran fuska ga fadar ta hanyar samar da ofishi ga Oluyin a Majalisa da karamin dakin taro.

“Oba Ajakaiye ya kuma yi murna da ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse guda biyar waɗanda yan asalin yankin suka ba da gudummawa, ya tallafa wajen ƙirƙirar LCDA da hedikwatarsa ​​a Iyin-Ekiti tare da samar da kayan sakatariyarsa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here